• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KORONA-JAMI’AR LAGOS TA UMURCI DALIBAI SU FICE DAGA DAKUNAN JAMI’AR

Jami’ar jihar Lagos ta umurci dalibai su fice daga dakunan jami’ar don labarin samun masu cutar annoba a tsakanin daliban.

Wata majiya ta shaidawa jaridar yanar gizo ta Premium Times cewa hukumar jami’ar ta umurci dukkan dalibai su koma gida don yanda a ka shiga zagaye na uku na annobar korona bairos.

Yanzu dai jami’ar ta yanke fara karantar da dalibai daga gida da hakan zai fara ranar 26 ga watan nan na Yuli.

Dama a Najeriya daga Lagos a ka fara samun annobar korona kuma a kan dauki wanda ya je jihar da fargabar yiwuwar samo cutar.

Rigakafi da wasu su ka samu ya rage mummunar fargabar yaduwar korona.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *