• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KORONA-GWAMNATIN NAJERIYA TA HANA TARON IBADA KO BUKI FIYE DA MUTUM 50

Gwamnatin Najeriya ta sake dakatar da taruka na ibada ko buki na fiye da mutum 50 don matakan yaki da cutar korona bairos.

Sanarwa daga kwamitin yaki da cutar ta ce kazalika an dakatar da duk shagali a kulob da filayen shakawatawa har sai yanda hali ya yi.

Hakanan an sake dawo da takaita zirga-zirga a Abuja ko birane daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Zuwa yanzu dai an yi wa fiye da kashi 60% na rukunin farko allurar rigakafin korona na Astra Zeneca cikin shirin tallafi ga kasashe masu tasowa mai taken covax.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.