• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KORONA-GWAMNATIN NAJERIYA TA AIYANA JIHOHI 6 DA ABUJA A YANKUNA MASU HATSARI

Gwamnatin taraiyar Najeriya ta aiyana jihohi 6 da babban birnin kasar Abuja a matsayin wajaje masu hatsari ga kamuwa da cutar annobar korona.

Shugaban kwamitin yaki da cutar Boss Mustapha ya baiyana haka a wata sanarwa da ke bukatar takatsantsan wajen dafifin jama’a a lokacin murnar idin babbar sallah.

Jihohi sun hada da Lagos, Ribas, Kaduna, Kano da Filato.

Wannan ya nuna an yi gargadin kar a gudanar da hawan sallah musamman a jihohin na arewa kamar Kano.

Hakanan an ba da shawarar gudanar da sallar jumma’a da sauran taruka a waje da dakunan ibada.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *