• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KORONA BAIROS-RIGAKAFI DA MODERNA DA ASTRA ZENACA NA NASARA-HUKUMAR LAFIYA MATAKIN FARKO

Hukumar Lafiya matakin farko ta Najeriya ta ce a na cigaba da yi wa ‘yan Najeriya allurar rigakafi da MODERNA da kuma ASTRA ZENECA.

Zuwa yanzu hukumar ta ce an yi wa mutum miliyan 3 ne rigakafin cikin kimanin ‘yan kasar miliyan 112.

Daraktan kididdiga na hukumar Dr. Abdullahi Bulama ya ce ba a samun yankewar alluran kuma a na fatar yi wa kashi 70% na ‘yan kasar rigakafin kafin a yi ajiyar zuciyar nasara.

Bulama ya kara da cewa kalubalen shi ne akwai iya wa’adin lokacin da alluran da a ka kawo daga ketare za su kammala aiki.

Shin zuwa yanzu za a iya cewa kamuwa da korona a Najeriya na karuwa ne ko kuwa a’a?.  Dr.Bulama ya ce cutar in an yi la’akari da sabon nau’in ta wato DELTA VARIANT to hakika ta na karuwa ne.

Shin me mutane ke cewa ne game da rigakafin tun da a na samun masu daridari da sahihancin allurar?.

Ra’ayin mutane ya rabu biyu tsakanin masu cewa sam-sam ba za su yi rigakafin ba don tsoron akwai illa da masu cewa su na da niyyar yi.

Hukumar lafiya matakin farkon ta ce ta na aiki kafada-da-kafada da hukumar yaki da yaduwar cutuka don kawar da korona.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *