• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KORONA BAIROS-FADAR ASO ROCK TA FIDDA SABBIN KA’IDOJIN SHIGA FADAR

Fadar Aso Rock ta fitar da sabbin ka’idoji ga duk masu ziyarar fadar don yaki da abun da a ka baiyana da cutar annoba ta korona bairos.
Mai taimakawa shugban kan labaru Garba Shehu wanda shi ma kwanan nan ya samu kan sa daga cutar, ya ce ka’idojin ba wai don gwamnoni ba ne, a’a ga duk mai shigowa fadar ce daga wajen ta.
Babbar ka’idar ita ce mai ziyara ya tsaya a nan kofar shiga a yi ma sa gwajin gaggawa na cutar gabanin ba shi damar wucewa.
Bayanan sun nuna akwai kayan aikin gwajin a bakin kofar kuma kyauta ne za a rika yi don haka ba maganar sai an biya.
Duk da haka akwai wasu mutane kalilan da a ka yafewa yin gwajin amma su din ma a na ba su kwarin guiwar su tsaya a yi mu su gwajin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *