• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KORONA: ALAMU NA NUNA NAJERIYA KA IYA KOMAWA HANA FITA DON CUTAR ANNOBA

Biyo bayan labarin kamuwa da cutar annoba da wasu daga ‘yan kwamitin yaki da cutar na shugaban Najeriya Muhammadu Buhari su ka baiyana, yanzu masu sharhi na cewa komai zai iya faruwa na yiwuwar sake komawa yanayin hana zirga-zirga.

Hatta shugaban kwamitin Boss Mustapha, ya na yanayin killace kan sa biyo bayan kamuwa da cutar da wasu ‘yan kwamitin su ka yi.

Najeriya na daga kasashe da ba sa daukar tsauraran matakan yaki da annobar duk da haka akwai takaituwar yaduwar cutar a tsakanin yankunan talakawa da ba sa mu’amala da masu yawace-yawace a kasashen ketare.

Babban kalubalen hana fita shi ne takaici da talakawa kan shiga na rashin wadatar abinci don akasarin su, sai sun fita buge-buge su kan kalato na cefane.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “KORONA: ALAMU NA NUNA NAJERIYA KA IYA KOMAWA HANA FITA DON CUTAR ANNOBA”
  1. I am sure this post has touched all the internet visitors, its really really fastidious paragraph on building up new web site.

Leave a Reply

Your email address will not be published.