• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KOGIN NILU-MASAR TA BUKACI SHIGA TSAKANIN MAJALISAR DINKIN DUNIYA KAN GINA DAM A HABASHA

ByNoblen

Sep 27, 2021

Masar ta bukaci majalisar dinkin duniya ta shiga tsakani don samun matsaya mai ma’ana tsakanin ta da kasar Habasha kan yunkurin Habasha na datse kogin Nilu don gina gagarumar madatsar ruwan samar da lantarki a kasar ta.
Masar na nuna matukar damuwa don yanda jama’ar ta su ka dogara da kogin na Nilu wajen noman rani da sauran su; kuma aikin madatsar ruwa da Habasha ke yi ka iya rage karfin ruwan da ke tahowa gefen Masar har zuwa Sudan.
Ministan harkokin wajen Masar Sameh Shoukry ya mika bukata ga majalisar dinkin duniya a ganawar sa da babban sakataren Antonio Guterres a birnin New York din Amurka.
Masar na samun kasha 95 na bukatun ruwan ta daga kogin na Nilu don haka ta ke fargabar aikin madatsar ruwan na Habasha zai rage yawan ruwan da ke gangaro zuwa kasar ta.
Tun 2011 Masar, Habasha da Sudan ke tattaunawa don samun yarjejeniya amma ina, don Habasha na shaukin cigaba da aikin samar da lantarkin ta ruwa mafi girma a Afurka.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *