• Thu. Sep 29th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KO RANA DAYA NA RIKE TAKARAR MATAIMAKIN TINUBU NA GODE ALLAH-IBRAHIM MASARI

ByNasiru Adamu El-hikaya

Jun 23, 2022

Mataimakin dan takarar jam’iyyar APC na shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu wato Ibrahim Kabir Masari ya ce ko rana daya taka a ka ba shi dama ya rike matsayin takarar ya godewa Allah.

Ibrahim Masari na amsa tambaya ne kan cewa an nada shi don rike kujerar ce kafin a nada ainihin wanda a ke son ya yi takarar.

Masari wanda tsohon sakataren walwala ne na APC ya ce amincewa da Tinubu ya nuna ma sa cikin jerin sunaye da a ka mika don ba da takarar mataimakin, na nuna ya gamsu da akidar sa a siyasa kuma ya zama abun yarda da zai ba wa marada kunya.

Wani abun da Masari ya baiyana da zai zama abun muhawara shi ne wannan karo ya ce musulmi-da-musulmi APC za ta yi a matsayin dan takarar shugaban kasa da mataimaki.

Mataimakin dan takarar ya ce la’akari da cancanta shi ya fi alheri ga ‘yan Najeriya maimakon bugewa da bambancin addin ko kabila “ai in ka duba matar Tinubu kirista ce kuma fasto ce ma” Inji Masari da hakan ke nuna ya aure ta ne don cancantar ta.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “KO RANA DAYA NA RIKE TAKARAR MATAIMAKIN TINUBU NA GODE ALLAH-IBRAHIM MASARI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.