• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KO MEYASA DALA KE CIGABA DA TASHIN GAURON ZABI A NAJERIYA?

Dalar Amurka na cigaba da tashin gauron zabi a Najeriya duk da barazanar cafke shugaban dandalin bayanan farashin canji na ABOKI FX da gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ya yi.
In za a tuna Emefiele ya zargi mai dandalin dan Najeriya mazaunin Burtaniya Olumide Oniwinde da tada farashin dala da sauran kudin ketare ta hanyar ba da farashin da ya wuce ka’ida a shafin na sa da mutane kan dogara da shi don sanin yanda canji ya kwana.
A daidai lokacin da Emefiele ya yi barazanar da ta sanya shafin ABOKI FX rufe sashin bayanan canjin Naira ya koma na kudin yanar gizo wato CRYPTOCURRENCY an kara samun tashin farashin dalar da wajen Naira 5 don in ba wani abu ne ya canja a wunin yau ba, dala daya ta kama Naira 565 ne a kasuwar bayan fage.
Godwin Emefiele da tuni ya dakatar da ba da dala ga kasuwac canji, na karfafa lalle mai son dala ya tunkari bankin sa da sahihan takardun tafiya, na magani ko kasuwanci don samun kudin bisa canjin gwamnati. Hakanan in ma bukatar mutum ta wuce mizani za a iya sanar da babban bankin don dubawa a biya bukatar mai bukata.
An shiga kasuwar canjin a Abuja an samu ‘yan canjin na cigaba da harkokin su cikin natsuwa da fatar gwamnati ta sauya tsari don cigaba da sako dalar maimakon dogaro ga masu fito da ita daga ma’ajiyar banki ko gida su na sayarwa don samun na kashewa.
Dan canji Jibrin Zakar ya ce ba mai son tsadar kuma su ma ‘yan canji na iya asara ko riba ga yanda dalar ba ta da tabbas.
Masanin tattalin arziki a Abuja Yusha’u Aliyu ya ce matakan na gwamnati kan kasuwar canji ba za su zama da illar gaske ba inda a gefe a na lura da gaskiyar wadanda kan samu dalar daga bankuna.
Ba a taba samun tashin dala a tarihi da ya kai wannan karo ba don ko lokacin da lamarin ya yi muni a wajajen 2015 farkon hawa mulkin shugaba Buhari, ta cilla zuwa N520 amma zuba dala a kasuwar canji ta sauko da ita zuwa kasa da Naira 400.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *