• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KO DA AN DAGE A RABA NAJERIYA TO A YI HAKAN A RUWAN SANYI-ZAUREN VOA

ByNoblen

Jul 14, 2021 , ,

Masu jawabi a taron wata-wata na ofishin muryar Amurka na Abuja sun baiyana bukatar duk matsawar da a ka yi ta masu son raba Najeriya don kafa kasar Biyafara ko Oduduwa to a yi hakan ba tare da tada fitinar da za ta kai ga zubar da jini ba.

Masu jawabin da su ka hada da Barista Mainasara Kogo, Injiniya Zakari Nguroje, Nastura Ashir Sharif, Maryam Mamman Nasir da sauran su, sun ce matukar akwai matsin lambar raba Najeriya, to kawai a kawo tsarin zaben jin ra’ayi kamar yanda a ka yi har a ka kafa Sudan ta kudu.

Masu jawabin sun ce matukar bukatar ba muradin siyasa ba ne don zaben 2023, to ya na da kyau ‘yan majalisa daga yankunan da ke son a rabe, su gabatar da bukatar gaban majalisa don daukar matakin a hukumance.

Sun kara da cewa ba wanda ya ke shakkar a raba kasa daga arewa, amma kar hakan kuma ya zama hanya ta cin mutunci da kisan gilla ga ‘yan arewa da ke zaune a kudu.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “KO DA AN DAGE A RABA NAJERIYA TO A YI HAKAN A RUWAN SANYI-ZAUREN VOA”
  1. Good day very cool blog!! Man .. Excellent .. Superb .. I’ll bookmark your website and take the feeds I’m satisfied to search out so many helpful info right here within the post, we need work out more strategies in this regard, thanks for sharing. . . . . .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *