• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KISAN GILLA NA KARUWA A YANKIN KUDU MASO GABASHIN NAJERIYA

Kusan kullum sai an samu labarin kai hari kan mutane a yankin kudu maso gabashin Najeriya inda miyagun iri kan yi kisan gilla kan wadanda ba su yi laifin komai ba.
Kisan gilla ga soja da matar sa a jihar Imo ya kara nuna nisan da miyagun irin da su ka yin a zubar da jini don cimma muardun su.
An fahimci cewa miyagun sun yi kisan gillar ne don huce haushi kan sojoji da su ke zargi da kai mu su hare-hare don haka tamkar sun rama ne.
A hankali yankin na juyewa zuwa mai mallakar ‘yan ta’adda da ke fakewa da neman kafa kasar Biyafara a jihohin kudu maso gabar don nuna gajiya da zama a cikin Najeriya.
Mugun nufin ‘yan bindigar na yawaita a jihar Abia, Imo da Anambra da a farko yak an shafi ‘yan arewa da ke sana’ao’I a jihohin.
Madugun ‘yan bindigar Nnamdi Kanu na hannun jami’an tsaron DSS ya na fuskantar shari’ar cin amanar kasa a gaban mai shari’a Binta Nyako ta babbar kotun taraiya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.