• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KISAN GILLA GA AHMED GULAK A OWERRI YA KARA NUNA YANDA WASU KE NEMAN WARGAZA NAJERIYA

Kisan gilla da ‘yan bindiga su ka yi wa tsohon mai taimakawa shugaba Jonathan kan siyasa Barista Ahmed Gulak da ‘yan bindiga su ka yi a Owerri jihar Imo na nuna yanda wasu su ka dage don wargaza Najeriya.

An ga gawar Ahmed Gulak cikin jini a yashe a gefen mota kirar Camry a gefen titi a Owerri, inda a ka kashe shi lokacin da ya kama hanyar filin jirgin sama.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna matukar kaduwa kan wannan kisan gilla, ya na mai alwashin kamo miyagun irin don fuskantar shari’a.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.