• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KISAN DEBORAH SAMUEL-‘YAN SANDA SUN KAMA DALIBAI BIYU

Biyo bayan kashe dalibar kolejin ilimi ta Shehu Shagari a Sokoto da daliban makarantar su ka yi, ‘yan sanda sun ba da labarin kama biyu daga cikin daliban.

Daliban sun zaro Deborah da karfin tsiya daga dakin tsaro na makarantar inda ta buya bayan kalaman cin zarafin Manzon Allah mai tsira da aminci, su ka kashe ta kazalika su ka kona gawat ra.

Deborah dai tun farko ta aika sakon sauti ne na aibanta Manzon Allah ta tura shafin makarantar na dandalin sada zumunta na Whatsapp.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Sanusi Abubakar ya ce za a kamo sauran daliban da a ka gani a faifan bidiyon kisan Deborah.

A shekaru da dama an taba samun irin wannan kisan a Kano lokacin da wani mai suna Gideon ya aibanta Manzon Allah, sai mutane su ka kashe shi da fille kan sa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.