• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KIMANIN MUTUM 20 SUN RASA RAN SU A HATSARIN MOTA A JIHAR OYO RANAR JUMMA’A

ByNoblen

Sep 11, 2022

Wani hatsari mai munin gaske na mota ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutum 20 a yankin karamar hukumar Ibarapa ta gabar a jihar Oyo kudu maso yammacin Najeriya.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya NAN ya ruwaito cewa motoci biyu da su ka hada da safa da mota kira SIEANNA sun yi taho mu gama inda kuma su ka kama da wuta.

Shugaban karamar hukumar Gbenga Obalowo ya ce ya jagoranci tawagar masu agajin gaggawa zuwa bigiren da hatsarin ya auku don taimakawa wadanda hatsarin ya rutsa da su.

Bayanai sun nuna cewa mutanen da su ka mutu sun kone har ta kai ga ba a iya gane gawar su.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
5 thoughts on “KIMANIN MUTUM 20 SUN RASA RAN SU A HATSARIN MOTA A JIHAR OYO RANAR JUMMA’A”

Leave a Reply

Your email address will not be published.