• Fri. Dec 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari...

KEDCO: BA A KORE NI DAGA SHUGABANCIN KEDCO BA-JAMILU GWAMNA

Shugaban kamfanin wutar lantarki na yankin Kano Jamilu Isiaku Gwamna ya musanta cewa an kore shi daga aiki.
An ga labaru a kafafen yanar gizo da ke nuna an sallami Gwamnan daga aikin bisa zargin almundahanar kudi.
Jamilu Gwamna wanda ke son takarar gwamnan Gombe a PDP, ya fito a wani faifan bidiyo ya na cewa ba yanda za a yi a kore shi daga kamfanin don ya na daga cikin masu manyan hannun jari.
Gwamna ya kara da cewa zai bar mukamin don lanuran siyasa, ya na mai zargin masu hamaiya da shi da yada labarin.
Jamilu Gwamnan dai bai tantance shin sauka ya ke son yi a ka fassara da kora da ya yi kaifi ko kuma ba za a iya korar sa kai tsaye ba tun da ya na da babban hannun jari a kamfanin.

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *