• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KAYODE MAI RAGARGAZAR BUHARI YA GANA DA BUHARI YA DAWO APC

T


Tsohon ministan jiragen sama Femi Fani Kayode da ya yi kaurin suna wajen sukar gwamnatin Buhari ya gana da shugaba Buharin a fadar Aso Rock, inda ya aiyana dawowa jam’iyyar APC.

Kayode wanda tun hawan shugaba Buhari mulki ya ke aibanta shi da kuma kushe al’ummar yankin arewacin Najeriya, ya shiga fadar Aso Rock da rakiyar shugaban rikwan APC Mai Mala Buni inda ya gaisa da shugaba Buhari don murnar dawowar sa APC daga PDP mai adawa.

Kayode ya ce duk abubuwan da su ka faru a baya ba su na nufin kiyaiya ba ne, amma kowa zai iya aiki daga inda ya ke ba tare da nuna bambancin addini, kabila ko siyasa ba.

Fani Kayode ya nuna ya dawo APC don muradun cigaban Najeriya a matsayin kasa daya.

Dawowar Kayode APC ta ba wa mutane mamaki musamman don ya taba cewa da ya dawo kazamar jam’iyyar APC gara ya mutu.

A gefe guda wasu masu sharhin na cewa ba su yi mamaki ba don hakan na nuna bakin ‘yan jari hujja daya ne na zama a madafun iko da gwara kan talakawa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
4 thoughts on “KAYODE MAI RAGARGAZAR BUHARI YA GANA DA BUHARI YA DAWO APC”
  1. whoah this weblog is wonderful i love reading your articles.
    Keep up the great work! You understand, lots of people are looking round for this
    information, you can aid them greatly.

  2. It’s really a nice and useful piece of info. I am satisfied that you shared
    this useful information with us. Please stay us up to date like this.
    Thanks for sharing.

Leave a Reply

Your email address will not be published.