Kawun shugaban Sham Bashar Al’Asad wato Rifaat Assad ya dawo gida bayan share shekaru 36 ya na gudun hijira.
Rifaat mai shekaru 84 ya gujewa kamu ne a Faransa bisa zargin almundhana shi ya sa ya dawo gida.
Kotu a Faransa ta samu Rifaat da laifin kwashe kudin Sham da gina gidajen alfarma a nan Faransa.
Tun a 1984, Rifaat ya fice daga Sham bayan yunkurin kifar da gwamnatin dan uwan sa marigayi Hafez Assad ya gaza nasara.
Jaridar Alwatan ta ce shugaba Bashar ya kau da ido kana bun da kawun say a aikata na yunkurin kifar da gwamnatin mahaifin sa, inda ya bar shi ya dawo Damaskas don kare shi daga shiga gidan yari a Faransa.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
This website was… how do you say it? Relevant!!
Finally I’ve found something that helped me. Thank you!