• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KATSINA 2023: ALH ABDULKARIM DAUDA KA FITO LOKACI YAYI

Wani shahararren dan siyasa Mutari AS Dikko wanda akafi sani da Ajiwa yayi kira da babbar murya akan Alh Abdulkarim Dauda Dauda ya fito a matsayin dan takarar gwamnan jahar Katsina a babban zaben shekara ta 2023.

Ajiwa yayi wannan kiran biyo bayan wasu kiraye-kirayen da ake yiwa Alh Abdulkarim Dauda kan ya fito ya nemi kujerar takarar gwamnan jahar, yana mai cewa ‘’ Alh Abdulkarim Tunda ka yarda da shiga jama’a to mun ce kafito siyasa, domin a halin yanzu ana son irin ka! Irin ka!! ake bukata, don munsan abinda zaka iya ne, to muna so kasa ma mana gyara, bakin abinda zaka iya gyara mamu”.

Haka ya cigaba da cewa ‘’ Mulkin nan anayi, kowa daidai karfinsa yakeyi, da daidai basirar shi tare da mashawartanshi, to muna so Alh Abdulkarim ya fito ya musal ta tashi basirar wanda tasha banban da wadanda suka faru a baya, lokaci yayi Alh Abdulkarim Dauda ka fito! Kabar boyo!.

Wannan kiran dai ba shine na farko ba, idan za’a tuna wasu ma daga yankin Funtua da kuma shiyyar Daura sunyi masa irin wannan kira don ya tsaya takarar Gwamnan Jahar Katsina a babban zaben badi 2023 in Allah ya kaimu, Allah yasa Alh Abdulkarim Dauda yaji wannan kira da suke masa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.