• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KASHE YAN KASUWA NA AREWA GUDA 7 A IMO YA HADDASA RUDANI

ByNoblen

Apr 5, 2021

Kisan gilla ga ‘yan kasuwa na asalin yankin arewa su 7 da a ka yi a jihar Imo ya jawo tada zullumin sake daukar matakan ‘yan kasuwa na dakatar da hulda da kudu.

Masu kisan gillar sun kashe ‘yan kasuwar a yankin Orlu da kuma Umuaka.

Lamarin ya auku ne tsakanin jumma’a da asabar.

Mahauta uku a Orlu na shirin tashi daga tukubar su, sai wasu a motar Sienna su ka zo su ka bude mu su wuta. Hakanan masu kisa sun shiga kasuwar Umuaka su ka bindige mutum hudu.

Duk mutanen da a ka kashen sun shafe shekaru su na gudanar da harkokin kasuwanci a yankin ba tare da wani sabani da jama’a ba.

Majiya ta nuna gwamnan jihar Hope Uzodinma ya nuna bacin rai da faruwar lamarin da zaiyana hakan da kiyaiyar siyasa kuma jami’an tsaro sun dau matakan samar da zaman lafiya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *