• Wed. Dec 1st, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KASHE MATAFIYA-BA MU YARDA A DAU DOKA A HANNU BA-SHEHU DAHIRU BAUCHI

Babban Shehun darikar Tijjaniyya a Najeriya Dahiru Usman Bauchi ya ce ba su yarda wasu su dau doka a hannu ta hanyar ramuwar gaiya bisa kisan gilla ga mabiyan sa ba a Jos, yayin da su ke komawa jihohin su bayan ziyarar da su ka kai ma sa a Bauchi.

Shehu Dahiru Bauchi wanda ke magana a taron manema labaru a Abuja, ya bukaci gwamnati ta ba da diyyar rayukan da a ka rasa.

Malamin ya ce duk hakkin kare rayukan jama’a na wuyan gwamnati don haka ta tabbatar da hukunta masu hannu a tare masu zikirin don hakan ya zama darasi ga masu niyyar aikata irin haka a nan gaba.

Shehu Dahiru Bauchi wanda ya yi ta’aziyya ga iyalan almajiran na sa da su ka rasa rai, ya ba da kwarin guiwar irin akasin ba zai sake faruwa ba.

Ba mamaki yanayin jihar Filato na ramuwar gaiya, ya sanya hukumomi a jihar kafs dokar hana fita dare da rana a yankin Jos ta arewa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *