• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KASHE DEBORA-GWAMNATIN SOKOTO TA AIYANA DOKAR TA BACI

Gwamnatin jihar Sokoto ta aiyana dokar ta baci don kwantar da zanga-zangar nuna bacin rai ga kama wasu daga cikin wadanda a ke tuhuma da kashe Debora Samuel a kolejin ilimi ta Shehu Shagari a Sokoto biyo bayan aibanta Manzon Allah Mai Tsira da Aminci da ta yi.
Masu zanga-zangar sun yi dafifi a fadar Sultan din Sokoto don neman masu ruwa ds tsaki su shiga tsakani wajen sako wadanda a ka kama.
‘Yan sanda sun hana masu zanga-zangar kutsawa cikin fadar don rigakafin abun da hakan zai haifar.
Akwai alamun wasu sun samu raunuka koma asarar rai.
Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya bukaci al’ummar su ba wa jami’ai hadin kai don wanzar da salama a jihar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “KASHE DEBORA-GWAMNATIN SOKOTO TA AIYANA DOKAR TA BACI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.