• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KASASHEN GABAR TA TSAKIYA NA ALLAH-WADAI DA AIBANTA MANZO DA NUPUR SHARMA TA YI

Kasashen musulmi na gabar ta tsakiya na cigaba da Allah-wadai da kalaman aibanta Manzon Allah da jami’ar labarum jam’iyyar gwamnati a Indiya Nupur Sharma ta furta a muhawarar gidan talabijin.

Da farko Saudiyya, Qatar da Kuwait ne su ka fara nuna fushin su kan Sharma amma yanzu labarin ya karade kasashen musulmi.

Tuni jam’iyyar ta gwamnati Bharatiya Janata BJP ta dakatar da Sharma daga aiki inda ta nuna kalaman sun sabawa manufofin ta.

Jakadun Indiya a gabar ta tsakiya na kokarin nesanta gwamnati daga kalaman Sharma, yayin da kiran kauracewa kayan Indiya ya fara karfi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.