• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KASAR SAUDIYYA TA JAJANTAWA PAKISTAN KAN IBTILA’IN AMBALIYAR RUWA

Saudiyya ta jajantawa kasar Pakistan kan ambaliyar ruwa da tayi sanadiyyar mutuwar daruruwan muta ne da raunata wasu da dama.
 
Sanarwar ta fito ne daga ma’aikatar kula da harkokin wajen saudiyya, Gwamnatin ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa tare da fatan samun sauki ga wadanda suka samu raunuka a ambaliyar.
 
A jiya juma’a firaministan Pakistan Shahbaz Sharif ya baiyana neman taimakon kasashen waje dan dakile ambaliyar ruwan da tayi sanadiyar tafka asarar rayuka, dukiyoyin al’uma da gurare masu muhimmanci a kasar.
 
A cewar sharif ambaliyar tayi muni kwarai idan aka kwatanta da ta 2010 saboda rashin kusan mutum 2000 da aka samu.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “KASAR SAUDIYYA TA JAJANTAWA PAKISTAN KAN IBTILA’IN AMBALIYAR RUWA”
  1. Can I simply just say what a relief to uncover somebody that really knows what they are discussing on the internet. You definitely realize how to bring a problem to light and make it important. A lot more people should check this out and understand this side of the story. I cant believe you arent more popular because you definitely have the gift.

Leave a Reply

Your email address will not be published.