Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya dau dabarar kalamai na neman hadin kan kasa a yayin aiyana neman tikitin APC.
Osinbajo daga kudu maso yammacin Najeriya, na ganin ‘yan Najeriya na iya zama ‘yan uwan juna.
Osinbajo ya kawo misalan yanda ke son mutanen garuruwan Najeriya na kudu da arewa za su daukar juna a matsayin ‘yan uwa, daga yanzu a zahiri wasu sassa ke zama doya da manja da juna.
Yemi Osinbajo duk da bai dauko batun masu son kafa kasar yarbawa ta Oduduwa ko ta Biyafara ba, ya zaiyana mafarkin ‘yan kasar ka iya daukar kan su uwa daya uba daya.
Ko da dai Osinbajo bai yi maganar uban gidan sa na siyasa ba Bola Tinubu ya bukaci goyon bayan ‘yan Najeriya.
Masanin harkokin siyasa Dr.Abubakar Kari ya ce matakin aiyana takarar Osinbajo ba sabon abu ba ne.
Magoya bayan Osinbajo na cewa ba shi nuna bambancin kabila ko yanki.
Bola Tinubu ya ce ba wani daga jama’ar sa a siyasa da ke takara ko ya kai matsayin yin takarar, don haka tamkar ya na cewa shi ne mai takarar daga kudu maso yamma.
KASA DAYA AL’UMMA DAYA – OSINBAJO

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
I was pretty pleased to discover this great site. I need to to thank you for your time for this particularly fantastic read!! I definitely appreciated every part of it and I have you book marked to see new stuff on your blog