• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KASA DA MAKO DAYA ZUWA AZUMIN RAMADAN 2021 KAYAN MASARUFI NA KARA TSADA

ByYusuf Yau

Apr 8, 2021

Kayan masarufi a kasuwannin Najeriya na kara tsada kasa da mako daya gabanin fara azumin watan ramadan na bana.

Wasu kayan sun tashi da wajen kashi 80% inda wasu kuma su ka yi karanci da ke nuna an boye su ne don samun ribar ribau.

Ba wani abun mamaki dama yanda kayan masarufi ke tsada gabanin fara azumin don lokacin ya zama wajibi ga masu azumi su nemi abinci mai inganci kuma kan kowane farashi za su tagaza su saya.

Da wannan ya nuna muhimmancin masu hannu da shuni su ninka taimako ga talakawa da sauran masu karamin karfi.

Hakanan da kai kayan buda baki masallatai da sayran wajajen gamwar jama’a.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *