• Fri. Dec 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari...

KARSHE IBIKUNLE AMOSUN YA SHIGA JERIN MASU NIYYAR TAKARAR SHUGABAN KASA A APC

Karshe dai tsohon gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun ya aiyana shiga jerin masu son takarar shugabancin kasa a jam’iyyar.

Amosun wanda ya sha arangama da tsohon shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole kan tsayar da wanda zai gaje shi a 2019, ya baiyana cewa zai inganta lamuran tattalin arziki da tsaro in ya samu nasara.

A takun sakar da Oshiomhole ta kai ga sai da Amosun ya tsayar da dan takarar gwamna a wata jam’iyya inda karshe dan takarar Oshiomhole na APC wato Dapo Abiodun ya lashe zaben.

Ibikunle Amosun na daga jerin ‘yan takara da dama da ke fitowa a APC daga kudu maso yammacin Najeriya, inda a jihar sa shi kadai ya zama na uku da ke son takarar bayan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da Pastor Tunde Bakare.

Wani abun lura shi ne daya daga ‘yan takarar gwamna Kayode Fayemi ya halarci taron aiyana takarar ta Amosun don biyan bashin yanda shi ma Amosun ya halarci aiyanawar ta Fayemi.

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *