• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KARSASHIN BABBAN TARON APC YA RAGU DON RASHIN GASA TSAKANIN MANYAN ‘YAN SIYASA

Karkashin gudanar da babban taron APC mai mulki a Najeriya ya ragu don rashin gagarumar gasa tsakanin manyan ‘yan takara.
Duk da dai ga manyan allunan hotunan ‘yan takara musamman na yankin arewa ta tsakiya, amma ba shige-da-fice na kamfen a zahiri da hakan bai rasa nasaba da raderadin tuni an san wanda zai zama sabon shugaban.
A na sa ran fiye da wakilai 4000 za su halarci taron da za a gudanar a dandalin taruka na EAGLE da ke tsakiyar Abuja.
A daf da ranar taron, ba mamaki a datse titunan tsakiyar birnin don samar da tsaro inda ya zama wajibi masu motoci su rika zabar wasu titunan gefe-gefe har sai an bude tsakiyar garin.
Rahotanni sun tabbatar da kame dakunan masaukan baki don sauke wakilan jam’iyyar da za su zo daga jihohin kasar 36 da kuma masu masaukin baki wato Abuja.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “KARSASHIN BABBAN TARON APC YA RAGU DON RASHIN GASA TSAKANIN MANYAN ‘YAN SIYASA”
  1. I was recommended this blog by my cousin. I am not sure whether this post is written by him as no one else
    know such detailed about my problem. You are wonderful! Thanks!

Leave a Reply

Your email address will not be published.