• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KARIN HAKO MAI BAI SHAFI FARASHI BA DON GANGAR FETUR TA CILLA FIYE DA DALA 70 A DUNIYA-YARIMA ABDULAZIZ

Ministan makamashi na Saudiyya Yarima Abdul’aziz Bin Salman ya ce karin hako mai ya zama alheri don yanzu gangar ta haura dala 70 a kasuwar duniya.

In za a tuna a baya gangar mai ta fadi kasa warwas da hakan ya kawo babbar barazana ga kasashe masu arzikin fetur.

Ministan ya baiyana a takaitaccen taron kungiyar kasashe masu arzikin fetur OPEC na tsawon minti 30.

Yarima Abdul’aziz ya ce Saudiyya na duba yiwuwar kara hako mai fiya da ganga miliyan 8.5 a duk wuni.

Duk da haka ministan ya yi hannun ka mai sanda na takatsantsan kan lamarin da sanya ido don dorewar nasarar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.