• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KARAWA TSOHON SUFETON ‘YAN SANDA WA’ADIN WATA UKU DAIDAI NE-KOTUN TARAIYA

Babbar kotun taraiya a Abuja ta yanke hukuncin cewa matakin da shugaba Buhari ya dauka na karawa tsohon babban sufeton ‘yan sanda wa’adin wata uku bayan cika shekarun ritaya, bai sabawa doka ba.

In za a tuna wani lauya a Abuja Maxwell Opara ya shigar da karar kalubalanatar karawa tsohon sufeton Muhammadu Adamu wa’adi da nuna hakan ya sabawa tanadin tsarin mulki.

Allah ya sa kafin cikar wata ukun, shugaba Buhari ya sauke sufeton ya nada sabo.

Alkalin kotun Ahmed Mohammed ya ce tsarin mulki da dokar ‘yan sanda ta yi magana kan yanda a ke nada babban sufeto amma ba ta yi magana kan kara ma sa wa’adi ba; don haka daidai shugaban ya kara wa’adin gabanin nada sabon sufeto don kar a zauna ba shugaban ‘yan sanda.

Maxwell Opara ya ce zai daukaka kara zuwa kotun daukaka kara.

Tun farko a shari’ar tsohon babban sufeton ya ce mulkin sa zai kare ne a 2024 bisa sabuwar dokar ‘yan sanda, ya na mai zaiyana wa’adin jagorancin babban sufeto kamar na mukaman siyasa ne.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *