Kimanin kwana daya ko biyu zuwa karamar salla wato sallar azumi, mutane musamman talakawa na ficewa daga Abuja don tafiya garuruwan su, su gudanar da idin a can.
Tashoshin mota na cike da fasinjoji inda su kan biya farashi mai tsada bisa yanda man fetur kan wuce Naira 165 a waje da Abuja.
Duk da yanda a ke fuskantar kalubalen tsaro, fasinjoji kan yi addu’a su kama hanya musamman hanyar Abuja zuwa Kaduna mai yawan samun akasin barayin mutane.
A na sa ran yin sallar a ranar lahadin nan ko kuma in watan ramadan ya cika kwana 3o a jira sai ranar litinin.
Gwamnatin Najeriya ta aiyana litinin da talata a matsayin hutu don karamar salla da kuma ranar ma’aikata.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
Thankyou for all your efforts that you have put in this. very interesting information.