• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KARA KORAR MINISTOCI ZAI FARFADO DA MARTABAR GWAMNATIN BUHARI

Masu sharhi na cewa rage karin ministoci fiye da biyu kacal da a ka sauke zai iya dawo da martabar gwamnatin shugaba Buhari da ta samu koma baya musamman gabanin zaben 2019.

Yawancin masu sharhi na cewa akwai ministocin da dabi’un su sammakal ne da wadanda a ka sauke na noma Sabo Na Nono da na wutar lantarki Saleh Mamman.

Ga Saleh Mamman ma wasu na yaba ma sa bisa fadar gaskiyar cewa aikin wutar lantarki daga Mambilla a kan takarda ne ba a fara wani abun a yi labari ba.

Hakanan wasu na cewa ya na da kyau a gaggauta cike gurbin ministocin da a ka sauke da wasu daga jihohin da su ke fito.

Wasu kuma na raderadin akwai wasu akalla ministoci biyar da su ka zama shafaffu da mai da ba sa taba a fadar Aso Rock saboda karfin fada ajin su.

Gabanin sauke ministoci biyu, gwamnatin Buhari ba ta taba wani garambawul ba tun da ta hau mulki a shekaru 6 da su ka wuce.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “KARA KORAR MINISTOCI ZAI FARFADO DA MARTABAR GWAMNATIN BUHARI”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *