• Wed. Dec 1st, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KAMAR AKASARIN ‘YAN AREWA NA BUKATAR ‘YAN AWAREN BIAFRA SU TAFI YANKIN SU

Alamu na nuna ‘yan arewa da dama sun dau matsayar a bar ‘yan awaren Biafra su kafa kasar su don a huta daga bakaken maganganun da su ke furtawa na kamar an danne su.

Kazalika hakan ka iya taimakawa wajen ceto rayukan ‘yan arewa da su ka hallakawa a yankin su, kona dukiya da kai hari kan jami’an tsaro da cibiyoyin tsaro.

Zai yi wuya a cikin masu ruwa a tsakin arewa a samu wanda ke marmarin a cigaba da dakatar da ‘yan awaren daga komawa yankin su don tamkar takaddamar ta kure hakurin al’ummar yankin.

Wani abun dubawa shi ne masu rajin awaren ba sa la’akari da tarin dukiya da ‘yan uwan su su ka jibge a yankin arewa.

A duk bakin wani titi idon jama’a a garuruwan arewa za ka taras da shangunan ‘yan kabilar Igbo shake da kaya na miliyoyin naira hakanan duk kungurmin kauyen da mutum ya shiga a arewa zai iya samun dan kabilar Igbo ya kafa shangon sayar da magani ko kayan mota da sauran su.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *