• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KALUBALEN TSARO YA SA FARIN JININ SHUGABA BUHARI YA RAGU-DAN BALKI KWAMANDA

Sanennen mai marawa shugaba Buhari baya a Kano Alhaji Abdulmajid Dan Balki Kwamanda ya ce tabarbarewar tsaro ya rage farin jinin shugaba Buhari a arewacin Najeriya.
A zantawa da a ka yi da shi ta wani shirin gidan rediyo, Dan Balki ya yi gargadin duk wanda ya Makala kan sa kan shugaba Buhari zai taimake shi a kamfen din 2023 ya sake dabara don guguwar Buhari ta lafa.
Kwamanda ya ce ba gwamnatin da ta ba wa matasa jari da ta kai yanda shugaba Muhammadu Buhari ya yi, amma rashin tsaro ya sa tallafin ba ya tasirin da za a ga amfanin sa a kasa.
Dan Balki ya ce wasu mukarraban shugaba Buhari sun tare kofa sun hana tsoffin magoya bayan shugaban samun ganawa da shi.
Masu sharhi tamkar sun yi ittifakin inganta tsaro shi ne kawai mafita ga kawo cigaba mai ma’ana a Najeriya da ke da dinbin arziki, amma yak an makale ba ya isa hannun talakawa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *