• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KALUBALEN TSARO: MASALLATAI SUN KARA DAGEWA WAJEN AL KUNUT A NAJERIYA

Masallatai musamman a arewacin Najeriya sun kara azama wajen addu’o’in alkunut don neman taimakon Allah ga tabarbarewar tsaro da ya shafi yawaitar satar mutane da hare-haren ‘yan ta’adda.

Azamar ta karu bayan kiran yin hakan daga shugaban kungiyar JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau a cikin umurnin da ya yi wa dukkan limaman masallatan kungiyar su dukufa ga addu’o’in na musamman don neman agaji daga ubangijin talikkai.

An ga manyan malamai irin Dr. Mansur Ibrahim Sokoto na nuna farin ciki ga wannan matakin da a kan yi a duk lokacin da a ka fuskanci irin wannan kalubale.

A na jin tashin addu’o’in daga masallatai musamman bayan sallar asuba inda mutane kan samu damar zama don yin Ibada bayan hutawa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “KALUBALEN TSARO: MASALLATAI SUN KARA DAGEWA WAJEN AL KUNUT A NAJERIYA”
  1. Awesome blog! Is your theme custom made or did you download it from somewhere?
    A design like yours with a few simple adjustements would really make my blog stand out.
    Please let me know where you got your theme. Kudos

  2. I am sure this piece of writing has touched all the internet visitors,
    its really really pleasant article on building up new website.

Leave a Reply

Your email address will not be published.