• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KALAMAN SHUGABA BUHARI SUN JAWO MUHAWARA

Kalaman da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kan daukar matakin dirar mikiya kan ‘yan awaren Biafra sun jawo muhawara tsakanin masu cewa hakan sara ne kan gaba da masu fargabar hakan ka iya murkushe su ko ‘yan uwan su.

Yanda a ke zaiyana sunan wadanda ke kashe ‘yan arewa a yankin Igbo da cewa ” ‘yan bindiga da ba a sani ba” ya juyo yanzu ga magoya bayan zubar da jinin zuwa shugaba Buhari na niyyar hallaka talakawa.

Kazalika wasu masu matukar mara baya ga zubar da jinin na nuna ‘yan awaren na zaune lami lafiya ba sa kashe kowa sai lokacin da shugaba Buhari ya tura sojoji su ka murkushe su ne ya sa su ka fusata da alwashin daukar fansa.

Gabanin nan ma su ma gwamnonin yankin ‘yan awaren na nuna su na bukatarva yi bincike kan wadanda su ka kashe hamshakin dan siyasar arewa Ahmed Gulak; maimakon su yi tir da ‘yan ta’addan da ke cigaba da aikata kisan.

Hakanan wasu na marmarin nuna Gulak ya rasa ran sa ne saboda rawar da ya taka a zaben fidda gwanin APC na jihar Imo a zaben 2019, inda kuma ba su faiyace ko wadanda su ke son su ce an dau hayar su, su yi kisan ‘yan awaren na Biafra da ke yawo da bindigogi kan tituna ko wasu ne daban.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.