• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KADUNA/KWADAGO-HAWA TEBURIN SULHU SHI NE ZABI MAFI A’ALA-SHEIKH BALA LAU

Shugaban kungiyar JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce za a iya warware rashin jituwa tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da kungiyar ‘yan kwadago cikin lumana ta hanyar hawa teburin shawara tsakanin sassan biyu.

Shehun malamin ya ce za a iya samun maslaha kan shirin gwamnatin jihar Kaduna ta Malam Nasiru Elrufai na rage yawan ma’aikata; ta hanyar zama waje daya tsakanin wakilan gwamnati da na kwadago da tsoma bakin dattawa, kwararru da shugabannin jama’a.

Ba za a bar jihar Kaduna a matsayin helkwatar arewa ta zama a cikin irin wannan rudanin ba don hakan ka iya fadada ya shiga wasu sassa ko jihohi.

Don haka Imam Bala Lau ya bukaci gwamnati da ‘yan kwadago su maida zuciya nesa ta hanyar warware takaddamar ta hanyar tattaunawa.

“ba za mu koma gefe mu na gani birnin mu mai daraja ya kasance cikin yanayin rudani ba. Don haka mu hadu don gano bakin zaren warware wannan takaddama ta hanyar da kowane bangare zai samu gamsuwa.”

Yayin da malamin ke lura da yanda jihar Kaduna da makwabta ke gwagwarmayar magance kalubalen ‘yan bindiga; ba daidai ne masu ruwa da tsaki su bari wata sabuwar kura ta taso ba.

A nan shugaban na Izala ya yi addua’ar neman taimakon Allah madaukakin sarki ga samun zaman lafiya mai dorewa, hadin kai, fahimtar juna da kwanciyar hankali a jihar Kaduna, yankin arewa da Najeriya gaba daya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.