• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KADUNA: AN SANYA DOKAR HANA YAWO DARE DA RANA A YANKIN KARAMAR HUKUMAR KADUNA TA KUDU DA CHIKUN

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana yawo dare da rana a yankin karamar hukumar Kaduna ta kudu da CHIKUN biyo bayan fasa rumbunan adanan abincin tallafin jinkai.

Kamar yanda ya faru a Filato, wasu mutane sun fasa rumbunan su ka yi awun gaba da kayan abincin.

Kwamishinan tsaro da lamuran cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya ce an umurci jami’an tsaro su damke duk wanda a ka samu ya na taka doka.

Hana yawon ya shafi Barnawa, Kakuri, da Television a yankin Kaduna ta kudu. A yankin Chikun kuwa ya shafi Maraban Rido, Sabon Tasha, Narayi da Romi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “KADUNA: AN SANYA DOKAR HANA YAWO DARE DA RANA A YANKIN KARAMAR HUKUMAR KADUNA TA KUDU DA CHIKUN”
  1. Hi, i think that i saw you visited my blog so i came
    to “return the favor”.I am attempting to find things
    to enhance my website!I suppose its ok to use a few of your ideas!!

Leave a Reply

Your email address will not be published.