• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KADDAMAR DA SARKIN DAWAN MATASA YA HADDASA YAMUTSI

Bukin kaddamar da Sarkin Dawan matasa na anguwar Maraba a jihar Nassarawa ya haddasa yamutsi inda wasu su ka dauka fitina ce ta tashi.

Rahotanni sun baiyana cewa matasa masu dawa sun fito da makamai gefen titi su na wasa da hakan ya jawo razanar wasu, su ka dauka hari a ka kawo mu su.

Musamman mutanen kudancin Najeriya da ba su san yanayin masu dawa ba, sun firgita ainun inda har lamarin ya kai makwabciyar anguwar Masaka.

Yanzu dai duk lamura sun daidaita bayan fahimtar cewa ba wani sabon tashin hankali ba ne.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.