• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KABUL YA FADA HANNUN TALIBAN YAYIN DA SHUGABA GHANI YA ARCE DAGA KASAR

ByNoblen

Aug 16, 2021 , ,

Karshe dai kungiyar gwagwarmaya ta Taliban ta kama babban birnin Afghanistan, Kabul, inda tuni shugaban kasar Ashraf Ghani ya arce daga kasar.

Kama birnin Kabul ya zo cikin ruwan sanyi ba tare da zubar da jini ba, inda ‘yan Taliban ke ba da kwarin guiwar tsaron rayuka, mutunci da hakkokin jama’ar kasar.

Wannan ya kawo karshen mamayar kasar da Amurka ta yi tsawon shekaru 29 da hakan ya ba da damar kafa gwamnatoci da su ka hada da ta tsohon shugaban kasar Hamid Kharzai da ya dade kan gado.

Bayanai na nuna mukarraban gwamnatin Afghanistan da ta fadi, da su ka hada da Abdullah Abdullah, Hamid Kharzai da tsohon shugaban rundunar mayaka masu jihadi wanda a yanzu ya ke jagorantar jam’iyyar Hezbul Islami Gulbuddin Hikmatyar, sun hada wani kwamiti na mika ragama cikin salama ga Taliban.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “KABUL YA FADA HANNUN TALIBAN YAYIN DA SHUGABA GHANI YA ARCE DAGA KASAR”
  1. You are so awesome! I do not suppose I have read through a single thing like this before. So good to discover someone with a few unique thoughts on this topic. Really.. many thanks for starting this up. This website is something that’s needed on the web, someone with some originality!

Leave a Reply

Your email address will not be published.