• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

JUYIN MULKIN SUDAN: BA A RABU DA BUKAR BA AN HAIFI-MASANIN SIYASAR SUDAN

ByNoblen

Oct 27, 2021
Ture gwamnatin rikwan kwarya ta shirya komawa mulkin dimokradiyya a Sudan da sojoji su ka yi bai zama wani abun mamaki bag a wadanda su ke bin siyasar Sudan.
 
Masu sharhi kan Sudan da su ka zauna shekaru da dama a Khartoum na cewa dama ture gwamnatin Elbashir ba shi ke nuna tsame hannun sojoji a mulkin kasar ta gabar Bahar Maliya ba.
 
Shugaban mulkin soja na Sudan Janar Abdel Fatah Burhan ya yi jawabin neman shawo kan mutan Sudan bayan ture majalisar rikwan kwaryar farar hula karkashin firaminista Abdallah Hamdok.
Burhan na nuna hukuma mai karfi za ta maye gurbi cikin adalci da sauraron ra’ayoyin al’ummar Sudan har ya kai ga lokacin zabe da tun farko a ka tsara a watan yulin 2023.
 
Da ya ke wannan ba shi ne yunkurin farko na kawar da ‘yan rikwan kwaryar ba, masu sharhi na cewa dabarar kwantar da tarzomar jama’a ne ta sa kawar da gwamnatin tsohon shugaba Omar Hassan Albashir amma ba wai don sojoji ko tsoffin sojoji na marmarin barin madafun iko ba.
 
Imran Adam Shu’aib wanda ya yi karatu da zama tsakanin babban birnin kasar Khartoum da Oumdurman ya ce zai yi wuya sojoji su sakarwa fara hula mara.
 
Shu’aib ya kara da cewa zai iya yiwuwa akwai mara baya na wasu kasashe masu karfi a duniya ga sauyin na Sudan.
 
In za a tuna sojoji sun kifar da gwamnatin Elbashir a ruwan sanyi a 2019 bayan gagarumar zanga-zanga, inda har a ka yi alwashin mika shi ga kotun duniya don fuskantar hukuncin fitinar Janjawid amma hakar hakan zai yi wuya ta tadda ruwa don tsarin tsohon sojan na bishiya mai dogayen jijiyoyi.
Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.