• Wed. Jun 29th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

JOSTIS NYAKO TA RAGE KWANA DAYA A TSAWON LOKACIN DA ZA A DAWO SHARI’AR NNAMDI KANU

ByNoblen

Dec 3, 2021 , ,

Jostis Binta Nyako ta babbar kotun Abuja ta rage kwana daya a tsawon lokacin dawowa kotu don cigaba da shari’ar shugaban ‘yan awaren Biyafara Nnamdi Kanu.
Jostis Nyako ta rage ranar daga 19 zuwa 18 ga watan Janairu badi.
A baya dai ficewar da lauyoyin Kanu su ka yi daga kotu don bara’a da hana wani lauya da ya zo daga Amurka shigowa da DSS su ka yi, ya sa kotun dage shari’ar zuwa wannan lokaci mai tsawo.
Biyo bayan bukata daga lauyan Kanu wato Ifeanyi Ejiofor, kotun ta bukaci hukumar DSS ta rika ba wa Kanu abinci mai dadi na Igbo da kuma barin sa ya na gudanar da addinin say a yahudawa.
A na tuhumar Kanu da laifin cin amanar kasa da ta’addanci ta hanyar haramtacciyar kungiyar sa ta IPOB mai neman raba Najeriya

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.