• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

JOE BIDEN YA LASHE ZABEN AMURKA NA 2020 INDA SHUGABA TRUMP KE CEWA AN TABKA MAGUDI

Dan takarar zaben Amurka na jam’iyyar Dimokrats Joe Biden ya lashe babban zaben Amurka da samun fiye da kuri’un jihohin raba gardama da a ke bukata.

Shugaba Donald Trump dai na nuna watsi da sakamakon da nuna an tabka magudi ne kuma zai kalubalanci sakamakon a kotu.

Tuni ‘yan jam’iyyar Dimokrats ke ta tsallen murnar sakamakon.Dama kakakin majalisar wakilai Amurka Nancy Pelosi da ke tsama da shugaba Trump ta aiyana Joe Biden a matsayin zabebben shugaban Amurka.

Joe Biden wanda shi ne mataimakin tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya kama hanyar shan rantsuwa a matsayin shugaban Amurka na 46 tun daga kan George Washington.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.