• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

JOE BIDEN YA KAMMALA ZIYARAR GABAR TA TSAKIYA

ByNoblen

Jul 17, 2022

Shugaban Amurka Joe Biden ya kammala ziyarar da ya ke gudanarwa ta wuni hudu a gabar ta tsakiya.
A lokacin ganawar sa da Yarima Muhammad bin Salman, shugaba Biden ya tabo batun kisan gilla da dan jaridan Saudiyya Jamal Khashoggi a karamin ofishin jakadancin Saudiyya a Istanbul din Turkiyya.
Biden ya zaiyana kisan da abun takaici.
Yarima Muhammad ya jaddada cewa Saudiyya ta hukunta wadanda su ka aikata laifin kuma a matsayin ta na kasa mai sanin ya kamata ta dau matakan da su ka dace.
Saudiyya ta ce kowace kasa kan iya yin kuskure hatta ita kan ta Amurka na yin kuskure.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.