• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

JIRGIN RWANDA ZAI KWASHI ALHAZAN UMRAH NA NAJERIYA 154

Kungiyar masu jigilar alhazan reshen Najeriya reshen Abuja ta bullo da wata dabara ta aiki tare wajen tattara kan masu niyyar umrah don tada jirgi guda su tafi tare.

Kungiyar ta yi nasarar harhada masu umrar 154 daga jihohin Najeriya da za ta yi amfani da jirgin kasar Rwanda a asabar din nan don tashi zuwa Saudiyya daga filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe.

Wannan na faruwa ne bayan rashin zuwa haji shekaru biyu a jere sanadiyyar annobar korona da hakan ya maida kamfanonin baya.

Ba mamaki samun damar zuwa umrah da Saudiyya ta bude zai iya kai wa ga nasarar zuwa hajjin bana.

Auwal Lalla shi ne shugaban kamfanin ALWADI da ke daya daga cikin masu jigilar ‘yan umrar, ya ce “za mu tabbatar da walwalar ‘yan umarar da kula da yanda za su rika samun shiga haramin Makkah don yin Sallah a zagayen dakin Ka’aba.”

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *