Hukumar sufurin jiragen kasa ta Najeriya NRC ta sanar da cewa za ta dawo da zirga-zirgar jirgi tsakanin Abuja da Kaduna a asabar din nan 23 ga watan oktoba.
In za a tuna hukumar ta takaita ko dakatar da zirga-zirgar biyo bayan dasa nakiya da barayin daji su ka yi kan titin dogon a yankin Rijana da ya zama tungar miyagun iri.
Wannan ya nuna hukumar ta gyara bigiren da ya gabce a sandaiyyar harin miyagun.
Da alamun masu hannu da shuni za su fara kaucewa shiga jirgin kasa su karfafa lamarin tashi ta jirgin sama tsakanin biranen biyu.
Duk haka har yanzu talakawa sun fi shiga mota su bi hanyar da ta ke tagwaye ne daga Abuja zuwa Kano duk da yanda a ke fargabar gamuwa da barayin.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀