• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

Jiragen Yaki Sun Yi Wa ’Yan Bindiga Luguduen Wuta A Sakkwato Da Katsina

ByAuwal Ahmad Shaago

Oct 8, 2021

Jiragen Sojin Saman Najeriya sun yi nasarar hallaka ’yan bindiga da dama tare da lalata maboyarsu a dazukan jihohin Sakkwato da Katsina.

 

A daya daga cikin hare-haren, jiragen yakin sun lalata sansanin wani dan ta’adda da ake kira ‘Gajere’ inda aka kashe yaransa 34, wasu kusan 20 kuma sun samu raunukan harbi. A Jihar Sakkwato dakarun sojin karkashin rundunar ‘Hadarin Daji’ sun kai hare-hare ne ta sama a dazukan Mashema, Yanfako, Gebe da kuma Gatawa a kananan hukumomin Isa da Sabon Birni.

Wata majiya ta soji  ta bayyana cewa an samu nasarar hakan ne a ruwan bama-bamai da suka yi ranar 5 ga watan Oktoba 2021, bayan sintirin da aka yi ta yi ta sama wanda ya gano wuraren da ’yan bindigar ke boyewa a cikin dazukan.

Rahotanni sun ruwaito mutanen da ke zaune a yankunan da aka kai hare-haren suna bayar da labarin yadda suka ga maharan na ta tserewa, yayin da wasu suka fake a wata makarantar firamare da ke kauyen Bafarawa.

A Jihar Katsina an gano yadda jiragen yakin Najeriya suka yi ta ruwan bama-bamai a maboyar maharan a dajin Rugu da ke da iyaka da Karamar Hukumar Kankara ta Jihar Katsina a tsakanin ranar 30 ga watan Satumba da 3 ga watan Oktoba, 2021.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “Jiragen Yaki Sun Yi Wa ’Yan Bindiga Luguduen Wuta A Sakkwato Da Katsina”
  1. F*ckin’ tremendous things here. I’m very glad to see your post. Thanks a lot and i’m looking forward to contact you. Will you kindly drop me a mail?

  2. Hello very cool blog!! Guy .. Excellent .. Wonderful .. I will bookmark your blog and take the feeds additionally…I am glad to find so many useful info right here in the post, we need work out more techniques in this regard, thanks for sharing. . . . . .

Leave a Reply

Your email address will not be published.