Jihohi 22 zuwa yanzu da akasari na arewa ne sun amince da shiga shirin gwamnatin Najeriya na kafa gandun daji don kiwon dabbobi.
Tsarin dai zai ba da damar bude dazuka ko shata inda makiyaya za su rika kiwo bisa kulawar gwamnati.
Tun watan Yuni a ka fara tsarin don kawo maslaha tsakanin manoma da makiyaya.
Shirin zai shafi samar da wajen ban ruwan dabbobi, makarantu da ma tsaro ga makiyaya.
Ba mamaki shirin ya zama wata hanyar samun kudin shiga ga jihohi.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀