• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

JIHAR ZAMFARA NA SHIRIN DAWO DA SADARWAR SALULA A LITININ DIN NAN

ByNoblen

Nov 29, 2021

Jihar Zamfara ta bi sahun jihar Kaduna wajen shirin dawo da sadarwar salula a litinin din nan.
Tuni jihar Kaduna ta dawo da sadarwar inda ta bar sauran dokoki na hana hawa babur da saida man fetur a jarka.
Zamfara ta rufe sadarwar waya tun watan satumba don shirin da jami’an tsaro su ka yi na yi wa barayin daji kofar rago.
Rufe sadarwar ta sanya jama’a shiga damuwa don rashin tasiri na zahiri kan barayin da su ka cigaba da miyagun laifuka.
Dama gwamnatin jihar ta dawo da sadarwar a babban birnin jihar Gusau da ya jawo farin ciki ainun a tsakanin ma’abota waya.
Alamu na nuna tasirin rufe sadarwar ba shi da yawa kan lamuran tsaro don a yankin Sabon Birni da Isa a jihar Sokoto an baiyana cewa barayin kan yi amfani da layin sadarwar Nijar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
9 thoughts on “JIHAR ZAMFARA NA SHIRIN DAWO DA SADARWAR SALULA A LITININ DIN NAN”
  1. We’re a group of volunteers and opening a new scheme in our community. Your web site provided us with helpful information to work on. You’ve done an impressive process and our whole neighborhood will be thankful to you.

Leave a Reply

Your email address will not be published.