• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

JIHAR SOKOTO TA RUFE LAYUKAN SADARWA A KANANAN HUKUMOMI 14

Don muradin yaki da ‘yan bindiga gwamnatin Sokoto ta rufe layukan sadarwar wayar salula a kananan hukumomi 14 na jihar.
Gwamnan jihar Aminu Tambuwal dama ya sanar da cewa ya bukaci ma’aikatar sadarwa ta rufe sadarwar kamar yanda a ka yi a Zamfara.
Tambuwal ya ce kananan hukumomin su ne mafi tsananin fama da illar ‘yan bindiga.
Gwamnan ya ce a sanadiyyar rufe sadarwa a Zamfara ‘yan bindigar sun garzayo Sokoto da cigaba da aikata miyagun laifuka.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *