• Wed. Jun 29th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

JIHAR BAUCHI TA SANYA KANANAN HUKUMOMI 4 CIKIN HALIN KOTA-KWANA

Gwamnatin jihar Bauchi a Najeriya ta sanya kananan hukumomin ta hudu cikin yanayin kota-kwana don kauda barar ‘yan ta’addan Boko Haram.

Wannan ya biyo bayan yanayin hare-hare ‘yan ta’addan a makwabciyar jihar Yobe, musamman a garin Geidam da ke kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar.

Sakataren gwamnatin jihar Sabiu Baba a taro da manema labaru, yace matakin ya zama wajibi don kare lafiya da dukiyar al’umma.

Baba ya bukaci jama’a kar su yi soko-soko da kula da lamuran tsaro don zai yiwu wasu daga ‘yan ta’addan sun kauro yankunan da a ke zubawa idon.

Tarob ya samu halartar jagororin tsaro na ‘yan sanda, soja da rundunar tsaro farin kaya ta DSS.

An gudanar da taron bayan taron tsaro da gwamnan jihar Bala Muhammad ya jagoranta.

Kananan hukumomin da lamarin ya shafa sun hada da Dambam, Darazo, Gamawa da Zaki.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.